Labarai
APC ta Jihar Zamfara ta Nuna Damuwa kan Zargin Lalata Allunan Tallace-tallace
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan zargin ci gaba da cirewa da lalata allunan talla da ke ɗauke da hoton Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na APC a Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, jam’iyyar ta ce ana ci gaba da aiwatar da waɗannan ayyuka tun wani lokaci, inda aka fara da kakabawa da kuma cire allunan APC a dukkan sassan jihar.
Sanarwar ta ce a baya jam’iyyar ta kai ƙorafi ga hukumomin tsaro domin dakatar da abin da ta bayyana a matsayin ayyuka na siyasa da gwamnatin jihar ke jagoranta ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ta hanyar lumana.
Sai dai APC ta ƙara da zargin cewa gwamnatin jihar ta sake komawa kan irin waɗannan ayyuka, tana zargin ta da amfani da hukumomin gwamnati, ciki har da Hukumar Tsare-Tsaren Birane da Yankuna ta Zamfara (ZUREP), wajen aiwatar da ayyuka masu tayar da hankali da ka iya haddasa ɗar-ɗar siyasa, musamman gabanin tarukan ƙungiyar jam’iyyar da kuma babban zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar ta kuma ce a ranar Laraba, jami’an hukumar sun yi yunkurin cire wani allon talla da ke ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa tare da na Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, da kuma Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, dukkansu tsofaffin gwamnonin Jihar Zamfara kuma jagororin APC.
An ce allon tallan, wanda yake gaban gidan zama na ministan a Gusau, ya tsira daga lalata ne sakamakon saurin sa-bakin jami’an tsaro da ke kula da gidan.
Jam’iyyar ta sake yin kira ga hukumomin tsaro a jihar da su tsoma baki domin hana ci gaba da irin waɗannan ayyukan lalata, waɗanda ta ce rashin girmamawa ne ga mukamin Shugaban Ƙasa da kuma cibiyoyin dimokiraɗiyyar ƙasa.
APC ta yi gargaɗin cewa rashin bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu girmamawa da karramawa da suka dace, a matsayinsa na jagoran ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ƙasa, ba za ta amince da hakan ba.
REL/AMINU DALHATU
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
