Labarai
An Fara Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na Bana
An fara bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na shekarar bana tare da jerin ayyuka daban-daban da suka haɗa da taron masu zuba jari, gasar tambayoyi ta makarantun sakandare, tsere-tsere, da nune-nunen al’adu da gargajiya, da sauransu.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Usman Zuru, wanda ya buɗe tarukan na rana, ya bayyana cewa waɗannan ayyuka abin tunawa ne na dindindin, yana mai cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta cancanci yabo bisa dawo da bikin bayan sama da shekaru biyar da dakatar da shi.
Alhaji Usman Zuru ya ƙara da cewa Majalisar Masarautar Argungu, a matsayinta na mai kula da gadon al’adu, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar shirin, inda ya yaba da rawar da Mai Martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, ya taka wajen sa ido da jagoranci a kowane lokaci.

Ayyukan da aka gudanar da rana sun haɗa da tseren raƙuma, tseren jaki, tseren dawakai, harbin baka, jefa majajjawa, da gasar polo ta ƙasa da ƙasa. Haka kuma, an bayyana cewa an kaddamar da tseren motoci, kekuna da babura tun da sassafe a birnin Abuja.
A cewarsa, mahalarta taron sun fito daga sassa daban-daban na cikin gida da wajen ƙasa, kuma za a raba kofuna da kyaututtuka ga dukkan waɗanda suka yi nasara daga matsayi na ɗaya zuwa na uku, ko dai a kuɗi ko kuma a kaya.
Bikin na shekarar 2026 an shirya shi ne domin nuna haɗin kai da kuma nasarar dawo da wannan muhimmin biki bayan dakatar da shi sakamakon wasu dalilai. Taron ya samu halartar jama’a masu yawa daga al’ummar Jihar Kebbi, jami’an gwamnati, da masu fatan alheri daga cikin gida da wajen ƙasa.
Taron ya haɗa ’yan Nijeriya daga kabilu, al’adu, addinai, ra’ayoyin siyasa da matsayi na zamantakewa daban-daban, inda suka taru cikin annashuwa, suna nuna haɗin kai, tare da jin daɗin kyawawan nune-nunen fasaha da al’adun gargajiya da bikin ya ƙunsa.
COV: SANI DUTSINMA
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
