Labarai
An Yi Kira ga Gwamnati da Ta Ɗauki Matakan Kare Al’ummomin Kan Iyaka
An yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su ƙarfafa tsaron kan iyaka ta hanyar bunƙasa arziki na bai ɗaya a tsakanin mazauna al’ummomin da ke kan iyaka.
Mataimakin Shugaban marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Mazabar Kwara ta Kudu, Sanata Lola Ashiru, ne ya yi wannan kira lokacin da mambobin Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), reshen Kwara, daga rukunin wakilan labarai, suka kai masa ziyarar ban girma a Offa.
A cewarsa, kyakkyawan tsarin kula da al’ummomin kan iyaka zai taka muhimmiyar rawa wajen rage ayyukan ta’addanci da laifuka a ƙasar nan.
Mataimakin Shugaban marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa ya bayyana cewa idan an tsare yankunan kan iyaka yadda ya kamata tare da bunƙasa tattalin arzikinsu, hakan zai zama gagarumin shinge ga aikata laifuka.
Sanata Ashiru ya ce wadata da arziki na da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa ƙarfin mutane na tsayayya da duk wata barazana ko tashin hankali, ko ta baki ko ta jiki.
Ya jaddada cewa dole ne a ba al’ummomin kan iyaka da kuma yankunan da ke nesa da birane kulawa ta musamman, yana mai bayyana su a matsayin layin farko na kariya daga barazanar waje.
Ɗan Majalisar ya yi kira ga gwamnatoci, musamman na jihohi, da su rungumi tsari mai ƙarfi na ci gaba da bunƙasa al’umma domin shawo kan matsalar rashin tsaro da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin Nijeriya.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
