Labarai
Nasarawa Ta Ƙaddamar da Shirin Dashe Itatuwa a Makarantu
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ƙaddamar da wani shiri na dashe itatuwa da nufin dasa itatuwa 100 a kowace makaranta a faɗin jihar.
Da take jawabi bayan kaddamar da shirin, Kwamishiniyar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta jihar, Dr. Magret Etaki Elayo, ta bayyana cewa ƙaddamar da shirin na makarantu wani ɓangare ne na aikin tsaftar muhalli na watan Janairu.
Dr. Magret Elayo ta ce wannan ƙoƙari na daga cikin manufofin gwamnatin jihar na dorewar muhalli da rage illolin sauyin yanayi, bisa tsarin manufofin gwamnatin tarayya.
Ta jaddada muhimmancin dashe itatuwa wajen yaƙar sauyin yanayi, hana zaizayar ƙasa, da kuma bunƙasa rayuwar halittu daban-daban.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa gwamnati ta riga ta ɗauki matakai na kula da itatuwan da za a dasa, tare da ƙarfafa malamai da ɗalibai su shiga wannan shiri domin kare muhalli.
Aliyu Muraki Lafiya
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
