Ilimi
Jami’ar Tarayya Dutse Za ta Rantsar da Sabon Shugabanta Ranar 10 ga Watan Fabrairu
Daga Usman Muhammad Zaria
Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta bayyana cewa za a rantsar da sabon Shugaban Jami’ar (Vice-Chancellor) da aka naɗa, Farfesa Ahmad Muhammed Gumel, zai gudana a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026 kamar yadda aka tsara.
Lauyan mai kare wadanda ake kara, Barrista Shamsu Ubale Jibrin ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Hakan na zuwa ne bayan ƙarar da Farfesa Abdulsalam Balarabe, ɗaya daga cikin masu neman kujerar Shugaban Jami’ar, ya shigar ta hannun lauyansa, inda yake ƙalubalantar tsarin zaɓen tare da roƙon kotu da ta hana Majalisar Gudanarwa da sauran waɗanda ake ƙara a shari’ar gudanar da bikin rantsarwar da miƙa mulki ga sabon Shugaban Jami’ar.
Barrista Jibrin ya ce a gabatarwarsa, ya gabatar da hujjoji masu ƙarfi tare da takardun shaidar gaskiya a gaban kotu, waɗanda ke nuna cewa an kammala tsarin zaɓen cikin tsari ba tare da karya daya daga cikin ƙa’idojin cancanta da aka ayyana a tallar da aka wallafa a jaridun ƙasa ba.
Ya ƙara da cewa lauyan Farfesa Abdulsalam Salam ya kasa gabatar da wata hujja a gaban kotu da za ta nuna cewa ba a bi ka’ida ba wajen naɗa sabon Shugaban Jami’ar.
Ya ce daga hujjojin da ya gabatar a gaban kotu, Farfesa Gumel ya cika dukkan sharuddan da ake buƙata don naɗa shi a matsayin Shugaban Jami’a, inda ya samu maki mafi yawa, tare da zama na farko a tantancewar da aka yi wa ‘yan takarar, sannan Majalisar Gudanarwa cikin hikimarta ta naɗa shi a matsayin Shugaban Jami’ar na huɗu.
Ya ce kotu ba ta amince da roƙon dakatar da rantsarwar ba, sai dai cikin hikimarta ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 23 ga Fabrairu bayan an kammala bikin rantsarwar.
A cewarsa, wannan wata nasara ce ga Majalisar Gudanarwa da Farfesa Gumel.
Barrista Jibrin ya bayyana cewa ya gabatar da hujjoji ingantattu don tabbatar da cewa Farfesa Gumel ya cika sharadin ƙwarewar aiki na shekaru 15 a jami’a a zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
