Labarai
Bayanan Da Aka Fitar Kan Jeffrey Epstein Sun Tayar Da Kura A Amurka
Wata ƙungiya ta waɗanda laifukan da attajirin nan na Amurka Jeffery Epstein da aka kama da ayyukan lalata suka shafa, sun soki ma’aikatar shari’ar ƙasar, bayan fitar da ƙarin takardu miliyan uku da suka shafi abubuwan da ya aikata.
Mataimakin babban lauyan gwamnati, Todd Blanche, ya ce sun cire sunayen mutanen ne don kare su, in ban da waɗanda watakila suka taimaka masa wajen yin abubuwan da ya aikata, kamar Ghislaine Maxwell.
Amma a cikin wata sanarwa, waɗanda abun ya shafa sun ce ana yayata sunayensu, wani abu da ke sake tuna musu irin cin zarafin da suka fuskanta a baya.
Epstein shahararren attajiri ne da ya yi abota da manyan masu faɗa a ji a duniya, ciki har da shugabannin ƙasashe da ƴan kasuwa, kuma ya rika yi masu kawalci da sunan lalata sa’ad da yake raye.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
