Connect with us

Labarai

Bayan Sauya Sheƙa: Gwamna Yusuf Ya Amince da Kafa Majalisar Dattawan Kano

Published

on

Daga Abdullahi Jalaluddeen

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa  APC,  inda ya jagoranci gagarumar sauya sheƙa a siyasar Jihar Kano.

Sauya sheƙar ta haɗa da mambobi 34 na Majalisar Dokokin Jihar, dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44, da kuma daukacin masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani babban biki da aka gudanar a dakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnatn Kano.

Da yake jawabi a taron, Gwamna Yusuf ya ce matakin sauya sheƙar ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da kuma tantance halin da jihar ke ciki a yanzu da burin da take da shi a gaba.

Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin yin aiki tare da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da nufin hanzarta ci gaban Kano tare da kawo ainihin amfanin dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar.

Bayan shawarwari masu zurfi kan makomar Jihar Kano, ni tare da mambobi 34 na Majalisar Dokoki, dukkan ƙananan hukumomi 44 da kuma dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa, mun yanke shawarar shiga jam’iyyar APC domin yin aiki da shugabanci mai hangen nesa na Bola Ahmed Tinubu,” in ji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya ce Ajandar sabunta kudurori ta Renewed Hope ta Shugaban Ƙasa ta fara haifar da sakamako mai kyau a faɗin ƙasar, yana mai jaddada cewa Kano ba za ta iya zama a gefe ba a lokacin da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya zai buɗe ƙarin damammaki ga al’ummarta.

Ya ƙara da cewa rikice-rikicen siyasa da faɗa ba su taimaka wa kyakkyawan shugabanci, yana mai bayyana shugabanci a matsayin hidima ga jama’a ba gasa ba.

Gwamnan ya tabbatar wa magoya bayansa cewa wannan mataki bai rage ƙoƙari da gudummawar dukkan waɗanda suka tsaya tare da shi a tafiyarsa ta siyasa ba.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su duba sauya sheƙar cikin adalci, yana mai jaddada cewa an ɗauki matakin ne da kyakkyawar niyya domin samar da ƙarin dama, musamman ga matasan jihar.

Haka kuma, Gwamna Yusuf ya sanar da amincewa da kafa Majalisar Dattawan Kano. Ya ce majalisar ba za ta kasance ta siyasa ba, kuma za ta zama cibiyar ba da shawara ga gwamnati domin inganta zaman lafiya, haɗin kai da kyakkyawan shugabanci a jihar.

A cewarsa, haɗin kai da Gwamnatin Tarayya zai taimaka wajen samar da yanayin siyasa mai tsafta da haɗin kai, tare da tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali na dogon lokaci.

 

Muna buɗe sabon shafi bisa ginshiƙin haɗin kai, kwanciyar hankali da shigar kowa. Ƙofofinmu a buɗe suke ga dukkan al’ummar Kano,” in ji gwamnan, yayin da ya yaba wa shugabancin APC bisa goyon baya da halartar bikin sauya sheƙar.

Manyan shugabannin APC da dama sun halarci taron, ciki har da tsohon Shugaban APC na Ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Karamin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane, Abdullahi Ata Fagge; Sanata Kawu Sumaila; Shugaban APC na Jihar Kano; da kuma dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44, tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

 

 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara