Labarai
Shugaban Kasa Zai Kai Ziyarar Aiki A TÜRKIYA
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja a Litinin, 26 ga Janairu, domin kai ziyarar aikin ƙasa zuwa Jamhuriyar Türkiye.
Manufar ziyarar ita ce ƙarfafa kyakkyawar alaƙar da ke akwai tsakanin ƙasashen biyu, tare da binciko ƙarin hanyoyin haɗin gwiwa a fannoni da suka haɗa da tsaro, ilimi, bunƙasa zamantakewa, kirkire-kirkire da harkar sufurin jiragen sama.
Idan za a iya tunawa, Shugaban Ƙasar Türkiye, Recep Tayyip Erdogan, ya kai ziyarar aiki zuwa Najeriya daga 19 zuwa 20 ga Oktoba, 2021.
A yayin ziyarar Shugaba Tinubu, ƙasashen biyu za su gudanar da tattaunawar siyasa da diflomasiyya kan muhimman batutuwan bai ɗaya da suka shafi kuɗi da harkokin kasuwanci, sadarwa, cinikayya da zuba jari.
Ajandar ziyarar za ta haɗa da taron manyan jami’ai daga ɓangarorin biyu, tare da sa hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a fannoni kamar binciken kimiyya, makamashi, haɗin gwiwar fasaha, kafofin watsa labarai da sadarwa, haɗin gwiwar soja da ka’idoji, da sauransu.
Haka nan, za a gudanar da taron kasuwanci, wanda zai haɗa ’yan kasuwa da masu zuba jari daga ƙasashen biyu, domin gano damammakin haɗin gwiwa a lokutan ziyarar.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo ƙasar nan bayan kammala ziyarar.
BELLO WAKILI
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
