Connect with us

Labarai

Zargin Juyin Mulki: Wata Ƙungiya Ta Bukaci Sakin Jami’an Soja da Aka Tsare Saboda Matsalolin Lafiya

Published

on

Wata ƙungiya mai taken Concerned Pro-Democratic Activists of Nigeria ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saki jami’an sojan da ke tsare bisa zargin hannu a wani yunkurin juyin mulki a Oktoban shekarar da ta gabata, har zuwa kammala binciken da ake yi kan lamarin.

Shugaban ƙungiyar, Comrade Yusuf Musa Dauda, ne ya bayyana wannan kira yayin taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.

Ya bayyana damuwa kan yadda wasu daga cikin jami’an da aka kama tun watan Oktoba ke tsananin rashin lafiya a yayin tsare su, ba tare da samun ingantaccen kulawar lafiya ba.

Comrade Yusuf Musa Dauda ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan hana iyalan jami’an damar ganinsu ko tattaunawa da su tun bayan kamunsu, ko aƙalla su san halin da suke ciki domin rage musu fargaba.

Ƙungiyar ta kuma yi Allah-wadai da tsawaita tsare jami’an sojan ba tare da gurfanar da su gaban kotu ko bin ka’idojin doka ba, a wani lokaci da ake ikirarin mulkin dimokiraɗiyya, inda ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani domin duba lamarin tare da sakin su idan babu tuhuma tabbatacciya a kansu.

A cewarsa:

“Hedikwatar Tsaron Ƙasa ta Najeriya, ta hannun tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, a ranar 4 ga Oktoba, 2025, ta sanar da kama wasu jami’an soja bisa zargin rashin da’a da karya ƙa’idojin aiki.

“Sojoji sun ce bincike ya nuna cewa korafe-korafen jami’an da aka kama na da alaƙa da yawan faduwa jarabawar ƙarin matsayi da kuma jin cewa aikinsu ya tsaya cak.

“Bayan wasu makwanni, jita-jita ta bazu cewa an kama su ne bisa zargin shirin juyin mulki, amma sojoji da gwamnati sun gaggauta musanta hakan.

“Duk da cewa muna yin Allah-wadai da duk wani yunƙurin kifar da gwamnati ta hanyar da ba ta dimokiraɗiyya ba, muna kira ga jama’a da kuma roƙon hukumomin da abin ya shafa da su yi adalci wajen duba wannan batu.

“Saboda haka, muna roƙon Gwamnatin Tarayya, Shugaban Ƙasarmu mai jin tausayin al’ummarsa, da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ba jami’an kulawar lafiya da ta dace.”

Ya kuma ƙara da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba da izinin jami’an da ke tsare su rika tuntuɓar iyalansu, domin rage musu damuwa da tabbatar da lafiyarsu da tsaronsu.

COV / Aliyu Muraki / Lafia

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara