Labarai
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Fara Girke Taransifoma 34 a Fadin Jihar
Gwamnatin Jihar Kwara ta fara girke taransifoma guda talatin da huɗu da ta saya a wurare daban-daban na jihar, a wani yunkuri na inganta samun wutar lantarki ga al’umma tare da ƙarfafa harkokin zamantakewa da tattalin arziki a jihar.
Kwamishinan Makamashi, AbdulAzeez AbdulGaniy, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Titin Orisunbare, kusa da Hanyar Egbejila, Asa-Dam, Ilorin, a lokacin da yake duba ɗaya daga cikin wuraren da aka amince a girke taransifomar.
Ya ce ayyukan girke na’urorin wutar sun riga sun fara a Shao, da ke Ƙaramar Hukumar Moro, da kuma wasu wurare daban-daban a fadin jihar.
AbdulAzeez ya bayyana aikin a matsayin wani bangare na ƙudirin gwamnatin jihar na inganta walwalar mazauna jihar da kuma ci gaban tattalin arziki zuwa sassa daban-daban na Kwara.
Ya kuma ba da tabbacin cewa al’ummomin da har yanzu ke jiran taransifoma za a saka su a matakai na gaba na shirin.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin na da cikakken ƙuduri na tabbatar da daidaito da kuma inganta yanayin rayuwa ga dukkan ‘yan jihar Kwara.
Daga cikin wuraren da suka ci gajiyar wannan shirin na girke taransifoma sun hada da: Caliphate Estate, Yankin Lubcon; Baba Ode Halbash Bakery, gaban Osin Aremu, kusa da Asa-Dam; Unguwar Ojodu, Baboko; Mandate, bayan Western Reservoir, dukkansu na cikin Ƙaramar Hukumar Ilorin Ta Yamma ta jihar, da sauransu.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
