Labarai
Shugaba Tinubu Ya Taya CPSO Usman Shugaba Murnar Cika Shekara 45 da Haihuwa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Kwamishinan ‘Yan Sanda, Usman Musa Shugaba, wanda shi ne Babban Jami’in Tsaron ‘Yan Sanda na Shugaban Ƙasa (CPSO), murnar cika shekara 45 da haihuwa.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai, Shugaba Tinubu ya yabawa Shugaba bisa ƙwarewa, aminci da jajircewarsa wajen aiki, inda ya bayyana hidimarsa a matsayin abin koyi da ke nuna ingantattun al’adun Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.
Shugaban Ƙasa ya jinjinawa ladabi, sa ido da sadaukarwa da CPSO ɗin ke nunawa wajen tsaron Fadar Shugaban Ƙasa da kare manyan cibiyoyin ƙasa, yana mai cewa rawar da yake takawa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali, tsari da amincewa a muhallin Shugaban Ƙasa.
“Ina yaba wa shekarunka na hidima ba tare da son kai ba da kuma sadaukarwar da ka yi, kuma ina gode maka bisa wannan muhimmiyar rawa da kake takawa cikin natsuwa amma mai matuƙar tasiri,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi wa CPSO fatan lafiya, ƙarfi, hikima da ci gaba da samun nasara a aikinsa da rayuwarsa ta sirri, yana mai fatan cewa shekarun da ke gaba za su kawo ƙarin manyan nasarori wajen yi wa ƙasa hidima.
A halin yanzu, Usman Musa Shugaba na aiki a matsayin Babban Jami’in Tsaron ‘Yan Sanda na Shugaban Ƙasa, matsayi mai matuƙar muhimmanci a tsarin tsaron Shugaban Ƙasa.
Bello Wakili
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
