Labarai
Tinubu Ya Yaba wa Hadiza Bala-Usman
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya mai ba shi shawara ta musamman kan daidaita manufofi kuma Shugabar Sashen Daidaita Ayyukan gwamnati, Hajiya Hadiza Bala-Usman, murnar cikarta shekara 50 da haihuwa, wadda ta cika a ranar 2 ga Janairu, 2026.
Sakon taya murnar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Malam Bayo Onanuga, ya fitar. Shugaba Tinubu ya bayyana Bala-Usman a matsayin jajirtacciyar ‘yar ƙasa mai kishin ƙasa, inda ya ce tarihin aikinta a hidimar jama’a ya cika da sadaukarwa, jajircewa da ƙwazo, tare da cikakken himma wajen bunƙasa ƙasar nan.
Shugaban ya jaddada cewa kusan shekaru talatin da Bala-Usman ta shafe tana hidimar jama’a sun ƙunshi darussa masu ɗorewa na shugabanci mai manufa, yana tuno da farkon aikinta a Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (Bureau of Public Enterprises), inda ta nuna hangen nesa mai zurfi da fahimta mai ƙarfi kan sauye-sauyen tsari da ake buƙata domin haɓaka tattalin arziƙi.
Ya bayyana jagorancinta da manyan nasarorin da ta cimma a Hukumar Kasuwanci ta Abuja (Abuja Enterprise Agency) da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (Nigerian Ports Authority) a matsayin muhimman ginshiƙai a aikinta, yana cewa ta karya shingaye, ta ɗaga ma’auni, tare da ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a harkokin mulkin jama’a.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba da gudummawar siyasarta, musamman rawar da ta taka wajen tsarawa da gina cibiyoyi a jam’iyyar (APC), wadda ya ce ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin cikin gida, ingancin gudanarwa da kuma ƙimomin dimokiraɗiyya.
A matsayinta na Mai ba da shawara ta musamman kuma Shugabar CRDCU a halin yanzu, Shugaban ya ce Bala-Usman na ci gaba da bambanta kanta ta hanyar ladabi a aiki, tsabtar tunani da mayar da hankali kan cimma sakamako, inda take bayar da gagarumar gudummawa wajen shugabanci bisa hujjoji da kuma aiwatar da Ajandar Renewed Hope.
Bello Wakili
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
