Connect with us

Labarai

Kotu Ta Amince Tsare Jirgin Ruwa Kan Safarar Hodar Ibilis Daga Brazil – NDLEA

Published

on

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Lagos ta ba da umarnin tsare wani jirgin ruwan dakon kaya, da matuƙinsa da sauran ma’aikatansa 20 bayan kama hodar iblis har kilogiram 25.5 a cikinsa a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa.

Umarnin ya biyo bayan wata takardar neman izini da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta shigar ne bayan jami’an hukumar sun gano hodar iblis din a cikin jirgin ruwan ‘yankasuwa, MV San Antonio, wanda ya isa Nijeriya daga Brazil.

Jami’an NDLEA, wadanda suka yi aiki bisa ga sahihan bayanan sirri, sun gano hodar iblis da aka ɓoye a cikin ramin jirgin a ranar 6 ga Disamban 2025, a cewar sanarwar hukumar a ranar Laraba.

Bayan da jirgin ya sauke kayansa gaba daya, an kama ma’aikatansa guda 21 waɗanda suka haɗa ‘yan kasashe daban-daban – ciki har da Rasha da Philippine da Ukraine da Azerbaijan – tare da miyagun ƙwayoyin da aka kama.

Wannan ci gaban ya zo ne makonni kadan bayan jami’an NDLEA sun kama wani jirgin ruwan, MV Nord Bosporus, wanda shi ma daga tashar jiragen ruwa ta Santos na Brazil ya taso, ɗauke da kusan kilo 20 na hodar iblis da aka ɓoye a ƙarƙashin kayansa a tashar Tekun Apapa a ranar 16 ga Nuwamban 2025.

Bisa la’akari da ƙa’idojin shari’a na duniya, NDLEA a ranar Jumma’a, 12 ga Disamban 2025, ta shigar da ƙara mai lamba FHC/L/MISC/1408/2025 a gaban Mai Shari’a Friday Nkemakonam Ogazi, tana neman umarnin a tsare jirgin da ma’aikatan jirgin har sai an kammala bincike da kuma shigar da ƙara.

Da yake yanke hukunci kan buƙatar, Alkali Ogazi ya amince da buƙatar kuma ya ba da umarnin tsare jirgin MV San Antonio da ma’aikatansa na tsawon kwanaki 14 da farko.

“An umarci kotu ta tsawaita tsare jirgin ruwan MV San Antonio wanda mai shigar da ƙara, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ke yi bincike a kai, na tsawon kwanaki 14 a shari’ar farko bayan kama kilogiram 25.5 na hodar iblis a cikin jirgin a ranar 6 ga Disamban 2025 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, har sai an kammala bincike da ko shigar da ƙarar laifuka da kuma gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji alkalin.

Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 29 ga Disamban 2025.

Da yake mayar da martani ga wannan ci gaba, Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce ƙwace kayan ya sake tabbatar da ƙudirin hukumar na hana kungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa da kuma abokan aikinsu na gida samun wani matsayi a Nijeriya.

Ya yaba wa jami’an rundunar dabarun Apapa bisa nasarar da suka samu a jere, yana mai bayyana su a matsayin shaida na ƙaruwar karfin hukumar da kuma ƙudurinta na wargaza hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi da ke fakon Nijeriya da kuma yankin Afirka ta Yamma.

Marwa ya kara da cewa NDLEA za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da abokan hulda na gida da na waje don tabbatar da cewa ba za a iya jure shan miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi ba a kasar.

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara