Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Rantsar da Sabbin Masu Bashi Shawara na Musamman Su 3

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria  

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin masu bashi na musamman guda uku da aka naɗa, a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar ga manema labarai, ya ce waɗanda aka rantsar su ne Alhaji Kabiru Hassan Sugungum, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Ƙasa; Ibrahim Ahmad Kwaimawa, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Dangantakar Masana’antu; da Ado Sani Birnin Kudu, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Ma’aikatan Gwamnati.

Yayin da yake rantsar da su, Gwamna Namadi ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin lokaci na ƙarfafa gwamnatinsa da kuma bunƙasa jihar.

A cewarsa, an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa cancanta, gaskiya, ƙwarewa da kuma tabbacin iya ba da gudummawa mai ma’ana wajen aiwatar da shirye-shirye da manufofin gwamnati.

Gwamna Namadi ya tunatar da su cewa hidimar jama’a amana ce, inda ya jaddada cewa rantsuwar da suka yi tana nuni da alkawari mai girma a gaban Allah da al’ummar Jihar Jigawa.

Yayin da nake taya ku murna kan kai wa wannan mataki, yana da muhimmanci a tunatar da ku nauyin da ke tare da wannan mukami. Hidimar jama’a amana ce, kuma rantsuwar da kuka yi a yau alkawari ne mai a gaban Allah da al’ummar Jihar Jigawa. A duk lokacin da ake irin wannan taro, nakan ji nauyin jagoranci sosai domin shugabanci daukaka ce kuma babban nauyi ne,” in ji Gwamnan.

Ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu da gaskiya, jajircewa da tawali’u, tare da fifita muradun jihar a kan komai.

Gwamnan ya kuma shawarce su da su ci gaba da ba da gudummawarsu  wajen yi wa jihar hidima, kamar yadda suka saba yi a tsawon shekaru.

Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa da kyakkyawar niyya da jajircewa, Allah zai musu jagoranci tare da su  taimaka musu wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.

Da yake mayar da martani a madadin sauran abokan aikinsa, Mai bada shawara na Musamman kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Alhaji Kabiru Hassan Sugungum, ya nuna matuƙar godiya ga Gwamna bisa amincewar da ya nuna musu.

Ya tabbatar wa Gwamnan da cikakkiyar biyayyarsu ga gwamnatinsa da Majalisar Zartarwar Jihar, tare da alƙawarin bayar da gudummawa yadda ya kamata wajen nasarar aiwatar da Ajanda 12 na Gwamna Namadi, daidai da Ajandar Sabunta kudurori ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Sugungum ya ce nauyin da aka ɗora musu ne ya ƙara musu karsashi, kuma da yardar Allah za su yi aiki tukuru domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, tare da tallafa wa hangen nesa na Gwamna na ganin Jigawa ta kara samun ci gaba.

 

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara