Labarai
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Sha Alwashin Wadata Al’ummarsa da Tsaftataccen Ruwan Sha
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya umarci a gaggawata gyaran bututun da suka hada tashar tacewa da samar da ruwa yankunan Dutsawa da Kantudu.
Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin da ake yawan fuskanta sakamakon lalacewar wutar lantarki da na’urar janareto, wanda ke hana jama’a samun ruwa yadda ya kamata.
Yayin da yake bayyana jimaminsa bisa wannan lamari, Dr. Muhammad Uba ya basu tabbacin cewa In Shaa Allahu matsalar ta zo karshe.

A cewarsa, majalisar ta kudirin aniyar yin duk mai yiwuwa domin magance matsalolin da ake fuskanta tare da tabbatar da samun isasshen tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.
Ya yi alkawarin tura dukkan kayan aiki da ake bukata domin ganin an warware matsalar.
Dr. Muhammad Uba ya kuma bukaci ma’aikatan hukumar ruwa ta Birnin Kudu da su kara jajircewa wajen kula da tsarin domin kauce wa sake fuskantar irin wannan matsala a gaba.
“Ina karfafa gwiwar dukkan ma’aikatan hukumar ruwa da su kasance masu lura, su zama masu saurin daukar mataki, kuma su kawar da duk wani cikas da zai hana cimma burin samar da ruwa mai dorewa a ko’ina cikin Birnin Kudu.”
Shugaban ya bayyana cewa aikin da ake yi a babbar tashar tacewa da samar da ruwan sha ya kusa kammaluwa.
A cewarsa, wannan aikin tare da gyaran bututun da ake yi yanzu na daga cikin babban shirin gwamnatinsa na inganta samar da ruwa a fadin karamar hukumar.
Wasu daga cikin mutanen yankin sun ce wannan mataki ya nuna jajircewar Dr. Uba wajen inganta muhimman ababen more rayuwa da kuma kyautata jin dadin al’ummar Birnin Kudu.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
