Connect with us

Labarai

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu da ƙalubalen da ta fuskanta a shekarar Taron manema labaran wani ɓangare ne na shirye-shiryen hukumar na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya. Barista Salisu Abdul ya ƙara da cewa, cin hanci babban abin da ke janyo koma-baya ne ga Najeriya a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a da tattalin arzikin ƙasa. A cewarsa, babban burin hukumar wacce aka kafa a watan Fabrairun 2024 shi ne ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar, tare da inganta gaskiya, ɗabi’a, da amana a harkokin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, da al’amuran zamantakewa da tattalin arziki.   Shugaban ya ce, a wannan shekarar hukumar ta shirya horo ga manyan ma’aikatan gwamnati da jami’anta, tare da wayar da kan jama’a kan rawar da kowa ya kamata ya taka wajen yaƙi da cin hanci. “Yayin da muke ci gaba da wayar da kai sosai, za mu ƙara haɗa kai da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci, da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, da jama’a domin mu fi mai da hankali wajen dakile cin hanci fiye da magance shi bayan ya faru,” in ji shi. Ya kuma ce, hukumar za ta rungumi fasahar zamani a ayyukanta don samun ingantaccen sakamako. Barista Salisu Abdul ya bayyana cewa, daga cikin shari’o’in 479, guda 110 sun shafi cin hanci da damfarar kuɗi, yayin da 375 suka shafi rikicin kadarori, sabanin iyali, da ma’amalar kasuwanci da ta ci tura, inda aka warware shari’o’i 107 cikin sulhu. Ya kara da cewa an dawo da fiye da Naira miliyan 385 da kadarorin da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyi, aka kuma mika su ga masu su. Sai dai ya nuna damuwa kan yadda alkalai ke tafiyar da shari’o’in a hankali, wanda ya bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke kawo cikas ga yaƙi da cin hanci a jihar. Shugaban Hukumar ya kuma nemi goyon bayan kafafen yaɗa labarai a yaƙin da ake yi da cin hanci, tare da yabawa Gwamna Umar Namadi bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar na yin aiki bisa cikakken ‘yanci ba tare da tsoma baki ba.

Labarai

Labarai16 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai19 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara