Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya

Published

on

Daga Shamsuddeen Mannir Atiku 

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar.

Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa.

Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai da kashi kashi 71 ga manyan ayyukan ci gaba, yayin da sama da naira biliyan dubu dari biyu da tamanin da shida daidai da kashi 29 za su tafi ga al’amuran yau da kullum.

Ya ce kaso mafi tsoka na ayyukan ci gaba ya mayar da hankali ne kan gina manyan muhimman ababen more rayuwa masu dorewa.

Rabe-raben kason sune: Ilimi ya samu kashi 25 bisa dari, sai  Ayyukan Gine-gine da Cigaban KarKarkashi ma kashi 25 bisa 100, Lafiya kashi 15 bisa 100; Noma da Samar da Abinci  kashi 11 bisa 100; Tsaro kashi 6 bisa 100; Ci gaban Zamantakewa kashi 5 bisa 100; Muhalli da Matakan Sauyin Yanayi kashi 4 bisa 100; sai Mulki da Gudanarwa kashi 5 bisa 100.

A nashi jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya ce kasafin kuɗin 2026 ya nuna sahihiyar manufa wadda ta ƙunshi faɗaɗa ababen more rayuwa a yankunan karkara, da habbaka kwazon ma’aikata da tabbatar da ganin dukkan al’ummomi suna cin gajiyar ci gaba mai ɗorewa da ya haɗa kowa.

Rt. Hon. Liman ya jinjina ga Gwamna Uba Sani da tawagarsa a bisa gabatar da kasafin da ya dace da hangen nesan gwamnatin da ke ƙoƙarin gina Jihar Kaduna mai  yalwar arziki.

Ya kuma gode wa gwamnan bisa samar da zaman lafiya, haɗin kai da sabunta kudurori a fadin jihar, tare da yabawa gwamnan bisa rashin yin katsalandan cikin harkokin majalisar wanda hakan alama ce dake nuna cikakken tsarin rabon iko da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen sa ido da daidaito tsakanin bangarorin gwamnati.

Labarai

Labarai7 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai10 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara