Labarai
Gwamnatin Jigawa ta Fadada Hanyoyi Tare da Dawo da Wutar Lantarki a Yankunan Taura
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta kammala bayar da kwangilolin gina kananan hanyoyi guda 15 da kudinsu ya haura Naira Biliyan 50 a bara.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin gina kananan hanyoyi na Chuwasu, Chukwaikwaiwa da Zangon Maje a karamar hukumar Taura ta jihar.
Ya bayyana cewa an bai wa wani kamfani kwangilar gina hanyar mai tsawon kilomita 26 da kudin ta ya haura Naira Biliyan hudu da rabi.
Malam Umar Namadi ya kara da cewa gwamnati ta kashe fiye da Naira Biliyan 10 wajen inganta hanyoyi a karamar hukumar Taura.

Saboda haka, ya bukaci kamfanonin da ke aiwatar da ayyukan hanyoyi daban-daban su tabbatar sun kammala ayyukan a cikin lokacin da aka kayyade.
Namadi ya kuma kaddamar da sabuwar fadar hakimin yankin Kwalam da Majalisar Karamar Hukumar Taura ta gina.
Ya bayyana jin dadinsa kan nasarorin da shugaban karamar hukumar ya samu wajen aiwatar da manyan ayyuka a yankin.
Umar Namadi ya kuma kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ga yakin Kwalam, wanda ya dade a cikin duhu fiye da shekaru 20.
Ya bayyana cewa sake hada wutar wani bangare ne na alkawurran yakin neman zaben sa na dawo da wuta a yankunan da suka jima babu hasken lantarki.

Gwamnan ya jaddada cewa samar da wutar lantarki a karkara da birane na daga cikin muhimman ginshikan tsarin mulkinsa mai kudurori 12, domin fadada damar samun wuta, karfafa tattalin arziki da rage kwararar mutane daga karkara zuwa birane.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun yaba wa Gwamna Namadi bisa dawowar wutar lantarki a Taura.
Namadi ya kuma duba aikin gyaran cibiyar kiwon lafiya ta farko ta Taura da majalisar karamar hukumar ta gudanar.
Karamar hukumar ta samar da gadaje da wasu kayayyakin asibiti a kokarinta na inganta ayyukan kiwon lafiya a cibiyoyin gwamnati.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
