Connect with us

Labarai

BUK Ta Horas Da Manoman Jigawa Kan Amfani Da Takin Gargajiya Don Inganta Gonaki

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Cibiyar Binciken Wuraren Shuka ta Jami’ar Bayero Kano (Centre for Dryland Agriculture – CDA) tare da hadin gwiwar shirin inganta harkar noma na Soil Values, sun horas da manoman Jigawa kan yadda ake samar da takin gargajiya  da kuma yadda ake amfani da shi domin farfado da ingancin ƙasa.

A yayin taron horas da manoma da aka gudanar a yankin Kunkuma na ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Dr. Bassam Abdulrahman ya bayyana cewa manufar shirin ita ce dawo da ƙimar ƙasar da ta lalace sakamakon dogon amfani da takin zamani.

 

Ya yi bayanin cewa ana samar da takin zamani ne daga sinadarai, kuma wasu daga cikin wadannan sinadarai na da haɗari, inda suke lalata ƙasar shuka sannu a hankali.

Dr. Abdulrahman ya kuma bayyana cewa cibiyar tare da hadin gwiwar shirin Soil Values ta horar da wasu manyan manoma (Lead Farmers) a Dutse, da Jahun, da Buji, da Kafin Hausa, da Birnin Kudu da Kiyawa kan yadda ake samar da takin gargajiya.

 

 

A cewarsa, an yi amfani da gonakin gwaji domin tabbatar da ingancin takin gargajiya, ta yadda manoma za su ga yadda takin ke mayar da sinadaran da ƙasa ta rasa bayan amfani da takin zamani iri-iri.

Shi ma a jawabinsa, Malam Mu’azu Salisu, ma’aikaci kuma malamin koyar da samar da takin gargajiya daga cibiyar, ya bayyana cewa sun yi samfurin gonar gwaji da nau’o’in taki daban-daban guda huɗu domin manoma su ga irin gagarumin tasirin takin gargajiya.

A nasa bangaren, Mataimakin Darakta na sashen bincike da kirkire-kirkire na CDA, Dr. Mustapha Bello, ya bayyana cewa an gudanar da taron horas da manoman ne domin nuna tsarin inganta kasar shuka domin  samin yalwar yabayan kuma mai inganci.

Ya ce sun kafa gonar gwaji inda aka yi amfani da takin zamani iri daban daban a wani bangare, sannan aka yi amfani da takin gargajiya a wani bangaren, domin manoma su ga bambanci da cigaban amfanin gona da aka shuka lokaci guda da takin daban daban.

Dr. Bello ya shawarci manoma su yi amfani da ingantattun irin shuka  hadi da takin gargajiya domin samun karin albarkar gona.

Wasu daga cikin manoman da aka horas, Bashir Bello daga Warwade a Dutse da Malam Amadu Mai unguwa daga Kukuma, sun bayyana farin cikinsu da sabbin ƙwarewar da suka samu tare da alkawarin fadada amfani da su domin ƙara yawan amfanin gona.

 

Sun yaba wa cibiyar saboda zaɓar al’ummar Kukuma domin gudanar da horon.

 

 

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara