Connect with us

Labarai

Mata 500 Za Su Amfana da Gwajin Cutuka Kyauta a Jihar Gombe

Published

on

Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku.

Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a hira da manema labarai a Gombe, a cikin shirin bikin Watan Wayar da Kan Jama’a game da Cutar Sankara.

Ta ce an shirya gwajin ne domin inganta gano cutar tun da wuri da kuma bada magani cikin lokaci, kasancewar cancer na nono da na mahaifa su ne manyan cututtukan sankara da suka fi addabar mata.

Dr. Hauwa Saurayi ta jaddada cewa gano cuta tun da wuri shi ne hanya mafi tasiri wajen rage mace-macen da ke da alaka da cutar sankara, tana jan hankalin mata da su daina jira sai alamun cuta sun bayyana kafin su nemi likita.

A nasa bangaren, Dr. Bawa Gift, Babban Likita (Senior Registrar) a Sashen Tiyata na Asibitin FTH Gombe, ya bayyana sankarar nono a matsayin cutar sankara da ta fi yawaita a tsakanin mata a duniya, tare da gargadi cewa karuwar yawan masu kamuwa da ita na kara zama babbar barazana ga lafiyar al’umma.

Ya ce wani binciken shekara ta 2022 ya tabbatar da cewa gano cutar da wuri da kuma kula da ita cikin lokaci na iya kara tsawon rayuwar marar lafiya, ko da ba a iya warkarwa gaba daya ba.

Dangane da sankarar mahaifa, Dr. Halima Faruk, Farfesa Mai Dangi (Associate Professor) a fannin Gynaecologic Oncology na FTH Gombe, ta bayyana cutar a matsayin “daga cikin cututtukan sankara mafi yawan yiwuwa a kare su amma mafi nauyi ga mata” a duniya.

Ta bayyana cewa kimanin sabbin mutane dubu 500 ke kamuwa da cutar sankarar mahaifa a duk shekara a fadin duniya, fiye da rabinsu na rasa rayuwa, musamman a kasashe masu karamin karfi irin su Najeriya.

Hudu Shehu Ibrahim/Gombe

 

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara