Labarai
Musulmi na farko ya lashe zaɓen magajin garin New York a Amurka
Zohran Mamdani ɗan jam’iyyar Democrat ya lashe zaɓen magajin garin birnin New York.
Mista Mamdani shi ne musulmi na farko da ya lashe zaɓen maganin garin a tarihin birnin.
Ɗan asalin Asiyan shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya zama magajin garin birnin mai muhimmanci a Amurka.
Hakan na zuwa ne a ranar da ake ganin jam’iyyarsu ta yi rawar gani a sauran zaɓukan da aka yi a wasu wurare a Amurka.
Mista Mamdani ya yi nasara a kan Andrew Cuomo na jam’iyyar Indifenda da kuma Curtis Sliwa na jam’iyyar Republican wanda ake gani shi ne zai zo na uku a zaɓen.
Waɗannan zaɓuka su ne na farko da ake gani kamar wani ƙalubale ne ga gwamnatin Trump.
Tuni dai Trump ya bayyana cewa ai ba da shi aka yi takara ba a zaɓen.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
