Connect with us

Labarai

FMC Birnin Kudu Ya Yi Bikin Ranar Maganin Kashe Radadi Ta Duniya

Published

on

Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana.

Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana.

Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846.

Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu ya ce taken ranar bikin na bana shi ne “Muhimmancin aikin kashe radadi a yanayin da ake bukatar agajin gaggawa” abin da yasa su ka yi amfani da wannan dama wajen shirya bita ga jami’an hukumar kiyaye hadura na karamar hukumar Birnin kudu kan hanyoyin lalubo numfashin wanda ya suma saboda bugun zuciya ko hadarin mota.

Da ya ke gabatar da bitar a aikace, Shugaban Sashen bada maganin kashe radadi lokacin aikin tiyata na asibitin gwamnatin tarayya dake Birnin kudu, Dakta Oliwe Augustus Chuks, ya ce akwai matakai da dama da ake bi wajen lulubo numfashin wanda ya yanke jiki ya fadi sumamme.

Yana mai cewar wadannan hanyoyi sun hada da tabbatar da yiwuwar bada agajin gaggawa lami lafia kafin taba jikin maras lafiya, da neman taimakon jama’a dan ceton rai da kuma danna kirjin wanda ya suma a hankali dan jini ya gudana daga zuciya zuwa kwakwalwa.

Yace sai kuma hura iska a baki domin bude kafofin da su ka toshe da motsa kashin mukamuki dan bude kofofin shan iska wadda hakan zai kai ga dadowar numfashi.

Sai dai kuma Likitan ya yi kira ga jama’a a tashar mota da makarantu da gidaje da su lakanci dabarun lalubo numfashin wanda ya suma domin kuwa wannan ilimi bai takaita ga likitoci kadai ba har ma da gamagarin mutane dan ceto rai kafin zuwa asibiti.

A nasa bangaren, Jami’in hukumar kiyaye hadura ta kasa na karamar hukumar Birnin Kudu, Malam Shu’aibu Uba Baba, ya bayyana jin dadin sa bisa wannan bita da ma’aikatan bada maganin kashe radadi lokacin aikin tiyata na asibitin FMC da ke garin Birnin Kudu su ka shirya musu.

Ya lura cewar, bitar za ta sake inganta abin da su ka sani wajen bada agajin gaggawa lokacin hadarin mota, inda ya roki ma’aikatan asibitin da su ware lokaci domin ci gaba da yi musu irin wannan bita nan gaba.

Taron ya samu halartar kungiyar kiyaye hadura ta masu yiwa kasa hidima, inda aka bada damar tambayoyi da bada amsa yayin da wasu daga cikin ma’aikatan hukumar kiyaye hadura da na masu yiwa kasa hidima suka jarraba matakan da likitocin su ka koyar da su muraran a aikace.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara