Connect with us

Labarai

NAPTIP ta Kama ‘Yan Safarar Mutane a Abuja, ta Kuɓutar da Mutane 24

Published

on

Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja.

Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.

Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello.

Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello.

Ya bayyana cewa a cikin waɗanda ake zargin akwai wani babban jami’in tsaro, wanda ke cikin masu safarar mutane a kudu maso yammacin Nijeriya.

Adekoye ya ce waɗanda aka kuɓutar ɗin yara ne da matasa waɗanda shekarunsu ke tsakanin  shekara 15 zuwa 26 waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano da Katsina da Oyo da  Ondo da kuma Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi da Sudan da Masar da Saudiyya da Bahrain da kuma Afghanistan.

Ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin cewa sai ta tabbatar an gurfanar da mahafinta a gaban kotu kan yunƙarin safararta da ya yi zuwa iraƙi, in ji jami’in.

Ya ƙara da cewa wata cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta ce mahafiyarta ce ta rinjaye ta ta yarda da cewa za ta tafi Turai domin yin aiki ta samu daloli.

 

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara