Fasaha
An sami Ci gaba a bangaren Sufuri – Farfesa Umar
Shugaban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura Jahar Katsina Farfesa Umar Adam Katsayal ya bayyana haka yayin zantawarshi da Radio Nigeria Kaduna.
A cewar Farfesa Umar Adam Katsayal kafin samun ‘Yan cin kai hanyoyin Mota hanya daya ne ba tagwayen hanyoyi ba sai bayan samun ‘yan cin kai aka fara samar da tagwayen hanyoyi tare ma da samun hanyoyin Mota da Suka hada garuruwa baya ga samun hanyoyin gadojin Mota na sama a manyan garuruwa da biranen kasa, hakama ta bangaren Filayen Jiragen Sama.
Shugaban Jami’ar Sufurin ya bayyana cewa kafin samun ‘yan cin kai sai a Birnin Ikko da Kano ake da tashoshin sauka da tashin Jiragen Sama da a yanzu kusan Jahohin wannan kasa ke da tashoshin sauka da tashin Jiragen Sama dama kokarin Samar da tashoshin Jiragen sama na dakon kaya.
Da ya juwa ta bangaren Sufurin tashoshin ruwa ya bayyana yadda ake dakon kaya daga wasu kasashe zuwa Nijeriya a tashoshin ruwa tare ma da samar da hanyoyin Jiragen kasa fiye da wadanda turawan mulkin mallaka suka bari da yanzu ma ake kokarin hada titin Jirgin kasa zuwa Jamhuriyar Niger baya ga tashoshin kan tudu da ake dako da sauke kaya.
Farfesa Umar Adam Katsayal ya bayyana ci gaba da aka samu a fannin Sufuri ta hanyar samar da Jami’ar Sufurin ta Gwamnatin Tarayya dake Daura domin inganta harkokin Sufuri a Nigeria da wannan Jami’a ita ce Jami’a irin ta ta farko a Nahiyar Africa.
A karshe Shugaban Jami’ar Sufurin ta Gwamnatin Tarayya dake Daura Farfesa Umar Adam Katsayal ya taya Shugaban kasa Bola Tinubu murnar cikar Nigeria Shekaru 65 da samun ‘yan cin kai da Mataimakinshi hadi da Shugabannin Majalisun Tarayyar Nigeria da Ministocin Sufuri da Ilmi a Tarayya Nigeria dama daukacin al’ummar Nigeria tare da kira ga ‘yan Kasa na ci gaba da yiwa Nigeria addu’o’in samun ci gaba da habakar tattalin arziki dama samun tsaro da zaman lafiya.
Ibrahim Idris Kaura Namoda/Kaduna
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
