Labarai
Hajjin 2025: Jami’an Kaduna Sun Sami Lambar Yabo Ta Kasa
Jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna sun sami lambar yabo ta kasa bisa namijin ƙoƙarin da suka nuna a aikin Hajjin shekarar 2025.
Kafar yada labaran aikin Hajji ta Independent Hajj Reporters (IHR) ce ta bayar da lambar yabon a wani taro da aka gudanar a Abuja.
Jami’an Hukumar Alhazan ta Kaduna da aka karrama sun haɗa da Hajiya Halima Lawal Babale, mai rikon mukamin Daraktan Sashen Gudanarwa da Kuɗi, da kuma Alhaji Surajo Umar, Shugaban Sashen Kula da Harkokin Kudi.
An yaba musu saboda sadaukar da kai da jajircewarsu wajen tabbatar da cewa Alhazan Kaduna sun samu kulawa, jagoranci da taimakon da ya kamata tsawon lokacin da suke kasa mai tsarki.
Babban Sakataren IHR na kasa, Ibrahim Mohammed, ya yaba da gagarumar nasarar da suka samu, inda ya bayyana su a matsayin abin koyi ga sauran jami’ai, domin sun taimaka matuƙa wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi.
Haka kuma, an karrama wasu jami’an hajji daga jihohi daban-daban da kuma kamfanoni masu zaman kansu da suka yi fice a aikin Hajji.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda Darakta-Janar na Gidan Rediyon Tarayya (FRCN), Muhammed Bulama ya wakilta, ya yaba wa IHR bisa ƙoƙarinta na inganta sha’anin gudanar da aikin Hajji.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin ci gaba da inganta walwalar alhazan Najeriya a ayyukan Hajji.
Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
