Connect with us

Labarai

Gamayyar Kungiyoyin  Jam’iyyar APC A Jigawa Sun Nemi A Ladabtar Da Sakataren Kudi Na Kasa

Published

on

Gamayyar kungiyoyin  jam’iyyar APC a jihar Jigawa sun yi Allah wadai da  ɗabi’ar sakataren kudi na jam’iyyar ta ƙasa, Alhaji Bashir Usman Gumel, suna bayyana halayensa a matsayin masu rarraba kawuna da barazana ga haɗin kan jam’iyya.

Yayin wani taron manema labarai a Jigawa, ƙungiyoyin sun zargi Bashir Gumel da halartar wani taron siyasa ba bisa ka’ida ba a garin Kafin-Hausa, a ranar 31 ga watan Agustn 2025.

Taron wanda aka ce an shirya shi ne domin girmama wani Zakari Kafin-Hausa, ana  zargin wasu ‘yan adawa sun halarta.

A cewar ƙungiyoyin, an yi kalamai masu zafi da cin mutunci ga Gwamna Umar Namadi da shugabancin APC na jihar a wajen taron.

Sun kuma zargi Bashir Gumel da yi wa wani mutum mubayi’a maimakon jam’iyyar APC, abin da ya haddasa tashin hankali har ya jawo raunika da asarar dukiya.

Kungiyoyin sun danganta hakan da shirin wayar da kan jama’a da Gwamna Namadi ya gudanar a ƙaramar hukumar Kaugama a wannan rana, wanda suka ce ya nuna sahihiyar jajircewar APC wajen kula da jin daɗin ‘yan ƙasa.

Duba da Sashe na 21 na kundin tsarin mulkin APC, ƙungiyoyin sun ce Bashir Gumel ya aikata ayyukan da suka ɓata sunan jam’iyya, ya kuma saba doka da umarnin jam’iyya, sannan ya ingiza kafa ƙungiyoyi na rarrabuwar kai.

Kungiyoyin sun bukaci shugabancin ƙasa na APC ya gaggauta bincikar wannan lamari, tare da ɗaukar matakan ladabtarwa da suka dace, domin irin wannan hali bai dace da wani babban jami’in jamiyyar na ƙasa ba.

Sun jaddada cewa ya zama wajibi  a tabbatar da ladabi da biyayya a cikin jam’iyyar domin kare haɗin kai.

Haka kuma sun ce bai kamata a tauye darajar tsarin jam’iyya da shugabanci musamman na jiha ba.

A cewar ƙungiyoyin, wannan lamari ya kunyatae da jam’iyyar ta APC,  tare da kawo barazana ga haɗin kan ta a Jigawa.

Sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamna Umar Namadi, suna yabawa da nasarorin cigaba da salon mulkinsa na haɗa kowa da kowa.

 

Wannan sanarwar ta samu sanya hannun shugaban haɗin gwiwar, Injiniya Sa’idu Ibrahim Uba, inda ƙungiyoyin suka yi alƙawarin ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyya a dukkan matakai.

 

Usman Mohammed Zaria

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara