Labarai
Hukumar NSCDC Ta Kama Masu Satar Kayayyakin Lantarki A Kano
Hedkwatar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da lalatawa da kuma satar kayayyakin wutar lantarki a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ga manema labarai a madadin kwamandan jihar, Shafi’u Abdulmumini.
Ya ce an cafke mutanen ne bayan samun sahihan bayanan sirri daga kungiyar sa-kai ta Hayin Da’e, da ke Hotoro, a ƙaramar hukumar Tarauni.
Abdullahi ya bayyana cewa an kama mutanen da wayoyin lantarki da aka lalata, waɗanda ake zargin sun cire ne daga wata na’urar tiransifoma da ke yankin.
Akasarin wadanda aka kama mazauna yankin ne da aka yi aika-aikar, wadanda shekarunsu suka kama da 18 zuwa 28.
“Bincike na farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun dade suna addabar mazauna Hayin Da’e, Farawa Kwanar Yashi, da Hotoro, ta hanyar fasa-kwauri, sata, da kuma lalata kayayyakin wutar lantarki,” in ji Abdullahi.
Kakakin NSCDC ya ce an riga an samu shaidar furuci daga hannun waɗanda ake zargin, yayin da bincike ke ci gaba domin cafke sauran abokan harkar su.
Ya tabbatar da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Shugaban hukumar, Shafi’u Abdulmumini, ya jaddada aniyar NSCDC wajen kare muhimman kayayyaki da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
Haka kuma ya bayyana cewa an ƙara tsauraran ayyukan sintiri da sa ido a duk fadin Kano domin masu aikata sauran laifuka.
Hukumar ta kuma yaba wa ‘yan sa-kai bisa bayanan sirri da suka bayar, wanda ya taimaka wajen kama batagarin, tare da kira ga al’umma su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro, da kuma bai wa jami’an tsaro hadin kai domin kawar da aikata laifuka a unguwanninsu.
ABDULLAHI JALALUDDEEN
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
