Labarai
Gwamnatin Kano Ta Horar Da Ma’aikata Kan Bunkasa Tattalin Arzikin Jihar
Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada aniyar ta na kara kuzari da kuma karfafa hanyoyin da za’a amfani Al umma wajen gudanar da ayyuka domin bunkasar tattalin arzikin kasa.
Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arzikina jihar, Honarabul Musa Sulaiman Shanono ya bayyana hakan a taron bita kan bunkasa tsarin kashe kudade na matsakaicin zango na 2026-2028 da aka shirya a kaduna.
A cewarsa, taron na da nufin kara fahimtar da masu ruwa da tsaki game da tsarin kasafin kudi da kuma duba ayyukan kasafin kudin jihar a shekaru 3 masu zuwa.

Musa Sulaiman Shanono ya yi bayanin cewa alfanun da ake son a cinma shi ne inganta tsarin kasafin kudi, gaskiya da rikon amana da kuma yadda ake raba kudaden jihar ga ma’aikatu, ta hanyar fifita kashe kudade bisa manufofin gwamnati.
Ya kara da cewa an zabo mahalarta taron ne daga dukkan ma’aikatu da sassa daban-daban na gwamnatin jihar Kano.
Kwamishinan ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayansa domin ganin an gudanar da taron cikin nasara.
Ya ce tallafin da ake bayarwa don inganta kwazon ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da kyautata jin dadin su da gwamnati mai ci ke yi ba zai misaltu ba.
Daga Abdullahi Shettima
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
