Connect with us

Labarai

Fitaccen jarumin Nollywood Amaechi Muonagor ya mutu

Published

on

Fitaccen jarumin Nollywood, Amaechi Muonagor ya mutu yana da shekara 62 a duniya, kamar yadda wani ɗan’uwansa ya shaida wa manema labarai.

Ya mutu ne ranar Lahadi bayan ya yi fama da ciwon ƙoda da ya sa ake yi masa wankin ƙodar, in ji rahotanni daga kafafen yaɗa labarai.

Ɗan’uwan jarumin Tony Muonagor da aka fi sani da Tony Oneweek, ya tabbatar da mutuwar ɗanfim ɗin

Mutuwar tasa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da ya nemi tallafin kuɗi domin yi masa dashen ƙoda a Indiya.

Da yawa cikin masu son fina-finansa sun yi ta jimamin rasuwarsa a shafukan sada zumunta.

Muonagor ya yi fina-finai da dama ciki har da shahararren fim ɗin nan na Aki da Paw Paw, ɗaya daga cikin fitattun fina-finan da ya taka rawa a matsayin mahaifin yaran.

Mutuwarsa ta zo ƴan makonni bayan da Najeriya ta yi rashin wani jarumin Nollywood John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu wanda shi ma ya buƙaci tallafin kuɗi domin neman magani.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai28 mins ago

Fasinjoji 85 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hatsarin Jirgin Sama A Senegal

Wani jirgin sama samfurin 737 dauke da mutane 85 ya tsallake rijiya da baya a filin jiragen sama na Dakar,...

Labarai49 mins ago

Za a Dauki Mataki Kan Masu Cin Zarafin Yan Aikin Gida

A wani mataki na kare hakkin ‘yan aikin gida da ma kare iyayen gidan da ake yi wa aikin daga...

Labarai1 hour ago

Majalisar Dattawan ta Amince da Hukuncin Kisa ga Masu Safarar Kwaya

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, bayan ƙudurin...

Labarai1 hour ago

Kotu ta Bayar da Belin Hadi Sirika kan Naira Miliyan 100

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Hadi Sirika ya musanta zargin aikata laifin almundahana da ya shafi kusan Naira...

Labarai1 day ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai1 day ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci2 days ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha2 days ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha2 days ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai2 days ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Mafi Shahara