Labarai
Gwamnatin Jigawa Na Aikin Tituna Na Miliyoyin Naira Don Bunkasa Aikin Gona
Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure.

Ya ce gwamnatin jihar ta bada kwangilar aikin ne akan kudi sama da Naira miliyan dubu 8 da miliyan 200 tare da wa’adin kammala aiki a watanni 18.
Kazalika, Malam Umar Namadi ya kuma bude aikin gina hanyar Farin Daba, Galo Babba zuwa Galo Karama da aka ba da kwangilar su kan naira miliyan dubu shida da miliyan 300.

Ya kara da cewar, aikin zai saukaka wa manoma kai kayan amfanin gonar su zuwa kasuwanni.
A don haka, Namadi ya tabbatar wa jama’ar jihar cewar gwamnatin sa na da burin samar musu da abubuwan more rayuwa.

A jawabin sa, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo S. Malam, yace aikin Dandi-Farin Daba-Gada an ba da shi ne ga wasu kamfanoni guda 2 tare da wa’adin kammalawa cikin watanni 24.
Injiniya Gambo ya kara da cewar, za a yi wasu ayyuka kamar gina magudanan ruwa da cika gefen hanya da sauran su.

Taron bude aikin ya samu halartar Mataimakin Gwamna Injiniya Aminu Usman, Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Said Ahmed, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum da sauran mambobin majalisar zartaswa ta jihar.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
