Connect with us

Labarai

Jihar Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Liberia Don Inganta Noman Shinkafa

Published

on

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karbi bakuncin Mataimakin Ministan Noma na Jamhuriyar Liberia, David Akoi, a wata ziyara ta musamman domin nazarin dabarun noman shinkafa a jihar, wadda ita ce kan gaba a fitar da shinkafa a Najeriya.

A yayin ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Dutse, Mista Akoi ya ce wannan ziyara za ta ba tawagarsa damar fahimtar dabarun noma da sarrafa shinkafa, samun horo a aikace, tare da koyo game da dukkan sassan harkar noman shinkafa. Ya bayyana cewa, wannan zai taimaka wa Liberia rage dogaro da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje.

A Liberia muna cin shinkafa safe, rana da dare. A shekarar 1979, an yi tarzomar shinkafa da ta kifar da gwamnatin Shugaba William R. Tolbert bayan yunkurin kara farashin shinkafa,” in ji shi. “Yanzu haka muna shigowa da kimanin kashi 70 cikin dari na shinkafar da muke ci.

Ya ce gwamnatin Liberia ta kuduri aniyar samar da aƙalla kashi 70 cikin dari na bukatar shinkafar cikin gida. Ya bayyana cewa Shugaba Joseph Boakai ya zabi Najeriya, musamman Jihar Jigawa, saboda irin ci gaban da ta samu a harkar noman shinkafa.

Mun zo ne domin koyo daga Jigawa yadda ta samu wannan nasara, da dabarun da ta yi amfani da su wajen shawo kan matsalolin noma.” In ji shi. “Manufarmu ita ce mu aiwatar da irin wannan nasara a kasarmu.”

Da yake mayar da martani, Gwamna Namadi ya yaba wa Liberia bisa zaben Jigawa, yana mai cewa wannan hadin gwiwa zai bai wa bangarorin biyu damar musayar dabaru da gogewa da za su amfani bangarorin noman su. Ya jaddada cewa noma ita ce ginshikin tattalin arzikin Jigawa.

A shekarar 2023, Jigawa na noman kadada 60,000 zuwa 70,000 na shinkafa. Amma a 2024, mun kai sama da kadada 200,000, kuma bana muna fatan kaiwa kadada 300,000. Burinmu shi ne mu samar da kashi 50 cikin dari na shinkafar da Najeriya ke bukata nan da 2030,” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa jihar na mai da hankali kan noman rani domin rage illar sauyin yanayi. “Muna gyara madatsun ruwa 10 da ke jihar, wanda hakan ke kara fiye da kadada 4,500 ga filayen noma,” In ji shi.

Don kara yawan amfanin gona, gwamnatin jihar ta samar da sababbin taraktoci 300 da  kayayyakin aikin su, injinan girbi 60, injinan shuka 150, da sauran kayan noma na zamani. Kowacce cikin mazabu 30 a jihar tana da akalla taraktoci 10 da ake ba manoma kananan haya a farashi rahusa rahusa.

Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa Jigawa za ta ci gaba da zuba jari a harkokin noma na zamani don karfafa sashen shinkafa, tare da bai wa Liberia goyon baya a yunkurinta na cimma wadatar shinkafa a cikin gida.

 

Usman Muhammad Zaria 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara