Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Yaba Wa Kungiyar NBA Bisa Inganta Manufofi Da Ka’idojin Aikin Lauya

Published

on

Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar.

A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya yaba wa shugabannin NBA bisa hadin kai da kwarewarsu wajen gudanar da aiki.

Na shafe watanni da dama ina bin diddigi da sha’awar yadda kuka kafa, tare da gudanar da ayyukan kungiyar  reshen jihar,  cikin haɗin kai da ƙarfafawa, inda ya zama wata gagarumar kafa wacce ke kare muradun aikin lauya da mambobin ƙungiyar a Jigawa  ma da wajen ta.” In ji shi.

Na yaba ƙoƙarinku na ganin yadda NBA reshen jihar ta samu nasara wajen inganta manufofi da ƙa’idojin da aka san ƙungiyar da su—wato kare doka, tabbatar da samun adalci ga kowa, ciki har da talakawa, da kuma tabbatar da gudanar da shari’a cikin sauƙi a jihar Jigawa.

Baya ga hulɗar aiki da zamantakewa, abin farin ciki ne ganin yadda irin waɗannan taruka ke taimaka wa wajen inganta bin ƙa’idojin aikin lauya da kuma ƙarfafa tattaunawa, ba kawai tsakanin lauyoyi ba, har ma da sauran muhimman masu ruwa da tsaki a harkar shari’a.”

Yayin bayyana gyare-gyaren gwamnatinsa a bangaren shari’a, Gwamna Namadi ya ambaci shirye-shiryen da suka haɗa da kafa Cibiyoyin Doka na Al’umma, gabatar da Zauren Sulhu, shirye-shiryen faɗaɗa Sashen Kare Haƙƙin Ɗan Kasa a kowace kotu, da sauran muhimman tsare-tsare.

Ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.

Ya bayyana fatan cewa tattaunawar za ta bayar da gagarumar gudummawa wajen kare ƙa’idojin  aikin lauya da kuma inganta gudanar da shari’a a jihar Jigawa.

 

Usman Mohammad Zaria

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara