Ilimi
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Mayar Da Dalibai 184 Da Suka Zo Hutu Daga Cyprus
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus.
Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, Babban Birnin Jihar.
A cewar sa, tuni rukunin farko na dalibai mata su 31 suka tashi ta filin jirgin saman ikko zuwa Istanbul inda za’a dauke su zuwa kasar Cyprus don fara sabon zangon karatu.
Alhaji Sa’idu Magaji wanda yake tare da daliban kafin tashin su, ya yaba da kulawar Gwamna Umar Namadi kan tallafawa daliban jihar domin ci gaba da karatun su.
Kazalika, ya nuna jin dadi da irin kulawar kwamishinan Ilmi mai zurfi ga daliban Jigawa dake karatu a ciki da kuma wajen kasar nan.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewar, daliban jihar Jigawan su 184 masu karatun aikin likita a kasar Cyprus sun zo hutu bayan kammala zango na biyu na karatun su kamar yadda gwamnatin ta yi alkawarin kawo su hutu idan sun kammala zango na biyu na karatun su.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
