Labarai
Ana Alhinin Tunawa Da Harin Nukiliyar Nagasaki Shekarau 80 Da Suka Gabata A Japan
Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani.
Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.
Harin na ranar 9 ga watan 1945 mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima.
An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan shekarar ta 1945, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin.
Bayanai sun ce a yau mutane sama da 2,600 daga ƙasashe sama da 90 sun halarci taron tunawa da wannan rana a bikin da aka gudanar da filin taro na garin Nagasaki.
Firai ministan ƙasar Shigeru Ishiba ya fara buɗe taron da jawabi da misalin ƙarfe 11:02 dai-dai lokacin da makamin ya dira a garin, a wani ɓangare na girmama waɗanda suka rasa rayukansu, kafin !bisani kuma aka rika kaɗa ƙarararwa don tunawa da ruhinsu.
An saki gwamman tattabaru da ke alamta zaman lafiya bayan da shugaban ya kammala jawabi, inda ya ce wannan taro ya shiga cikin kundin tarihin ƙasar wanda za’a gajeshi ƴaƴa da kakanni.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
