Labarai
Tinubu Ya Umurci A Bada Kulawar Lafiya Kyauta Ga Tsofaffin Ma’aikata Masu Karamin Fansho
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare da zai taimaka wa rayuwarsu.
A wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi ƙarancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma’aikata mafi rauni a tsarin CPS.
Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom), Ms. Omolola Oloworaran, ta gabatar wa Shugaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya kuma umurci Daraktar Janar ta PenCom din da ta gaggauta warware matsalar fanshon ’yan sanda da ta daɗe tana ci gaba, yana mai jaddada cewa ’yan sanda samar da tsaro a ƙasa suna da hakkin samun fansho cikin mutuntawa da kwanciyar hankali.
Daraktar Janar din ta kuma sanar da Shugaban ƙasa yadda ake ƙoƙarin kare darajar asusun fansho duba da hauhawar farashi da matsin tattalin arziki, da kuma shirin kaddamar da tsarin ba da gudummawar fansho da kudin waje domin bai wa ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar shiga tsarin fansho.
Shugaba Tinubu ya nuna cikakken goyon bayansa ga waɗannan gyare-gyare, yana mai sake jaddada aniyar gwamnatinsa na bunƙasa ci gaba mai ɗorewa da kare rayuwar talakawan Najeriya.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
