Connect with us

Kasuwanci

An Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Kaddamar Da Aikin Hanyar Firji Da Ta Ratsa Mazabu Bakwai

Published

on

An bayyana kaddamar da aikin hanyar Firji zuwa Guntai zuwa Buntusu ta wuce zuwa Dan Abzin mai nisan kilomita 29 da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa yayi a matsayin wani muhimmin ci gaba da aka dade ana daku a yankin.

Dan majalisar dokokin jihar Jigawa Mai wakiltar mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Gwiwa.

A cewar sa, al’ummar karamar hukumar Gwiwa za su dade su na tunawa da gwamnatin Umar Namadi bisa kaddamar da aikin wannan hanyar wacce za ta ratsa mazabu bakwai ta kuma hadu da karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina.

Ya kuma bayyana cewar manoma da ‘yan kasuwa na shan wahala shekara da shekaru musamman a yankunan Guntai da Buntusu wajen isa kasuwanni saboda matsalar hanya.

Alhaji Aminu Zakari ya bayyana amannar cewar idan aka kammala ta, wannan hanyar za ta bawa jama’ar mazabu bakwai damar kewayawa garuruwan yankin cikin sauki domin cin kasuwa da zuwa asibiti da ma sada zumunci.

Da ya ke tsokaci dangane da taron Gwamnati da Jama’a da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta, Aminu Zakari ya ce taron ya kasance na kafa tarihi bisa la’akari da muhimman abubuwan da su ka wakana kamar na kaddamar da aikin hanyar Firji da hanyar burji da Kuma gyaran asibitin Gwiwa da karamar hukuma ta yi.

Kazalika, Dan Majalisar ya godewa Gwamna Namadi da mataimakin sa da shugaban majalisar dokoki da sakataren gwamnati da shugabannin jam’iya da sauran masu ruwa da tsaki bisa kasancewa tare da al’ummar karamar hukumar Gwiwa a ranar taron.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara