Connect with us

Labarai

Kwalejin Koyar Da Aikin Jinya Ta Jigawa Za Ta Fara Bada Shaidar Babbar Difiloma

Published

on

Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025.

A jawabinsa wajen taron kaddamar  da daliban,  kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin sa na farko daga samun wannan mukami shi ne batun kafa hukumar Gudanarwar Kwalejin da sake fasalin Kwalejin, wanda hakan ya bada damar tantancewa da kuma samun amincewar Cibiyar kula da makarantun aikin Jinya ta Najeriya.

Yana mai cewar, daukar wannan mataki ya bada damar kara yawan dalibai da Kwalejin take dauka daga 120 zuwa 240, wanda hakan zai bada damar yaye dalibai masu yawa.

A cewarsa, jihar tana da ma’aikatan jinya 1,669 wanda ke nuni da gibin 1,883 in aka kwatanta da bukatar irin wadannan ma’aikata 3,552 domin kula da marasa lafiya a asibitoci.

Dr Kainuwa ya kuma taya murna ga tsangayoyin Kwalejin da ke Babura da Birnin kudu bisa kyakkyawan sakamako da suka samu a jarrabawar da ta gabata, inda su ka zamo kan gaba a tsakanin jihohin kasar nan.

Ya bayyana kiwon lafiya a matsayin kan gaba cikin kudurorin Gwamna Malam Umar Namadi guda 12, yana mai jaddada aniyar gwamnati na cigaba da bada kulawa sosai ga harkokin lafiya wanda yanzu haka ana inganta matsakaitan asibitoci 181 da kayan aiki da sauransu.

A jawabin shugaban Hukumar Gudanarwar Kwalejin Malam Salele Abdul, ya bukaci iyayen dalibai da kada su saki hannu bayan samun guraben karatu a kwalejin, domin kuwa akwai bukatar cigaba da ba su kulawa domin su kai ga nasara zuwa karshen karatunsu.

Malam Salele Abdul ya bayyana kwamishinan lafiya Dr Muhammad Kainuwa a matsayin Garkuwan Aikin Jinya bisa nasarorin da aka cimma a lokacinsa.

Kazalika, ya godewa wakilan hukumar gudanarwar da shugabannin Kwalejin bisa gudummawar da su ke bayarwa ga cigaban harkokin kealejin.

Tun da farko a jawabinsa, shugaban Kwalejin koyar da Aikin Jinya ta Jihar Jigawa, Malam Garba Adamu, wanda ya bayyana kudurinsa na ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa, ya kuma baiwa iyayen dalibai tabbacin horas da ‘ya’yansu kan doron Ilimi da kyakkyawar tarbiyya.

Daraktar Kwalejin Aikin Jinya Hajiya Rasheeda Musa Ya’u ta gabatar da sabbin daliban 116 maza da Mata ga Magatardar Kwalejin Malam Muhammad Sale Korau wanda ya lakana musu rantsuwar kaddamarwa.

Shima a jawabinsa, shugaban kwamatin shirye shiryen taron kuma shugaban sashen koyar da Aikin Jinya na kwalejin Malam Abubakar Garba Muhammad, ya ce bikin kaddamar da daliban na daga cikin sharuddan Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’oi da Manyan Makarantu ta Kasa wato (JAMB) domin fara karatun Difloma ta kasa da Babbar Difloma ta kasa a fannin aikin jiyya.

Ya kuma godewa dukkan wadanda suka bada gudummawa wajen samun nasarar taron.

Sakataren kungiyar ma’aikatan Jiyya ta kasa reshen jihar Jigawa Comrade Nurse Kamal Ahmad ya isar da sakon shugaban kungiyar ga taron, yayin da mukaddashin shugaban sashen kula da ayyukan jiyya na ma’aikatar lafiya Nurse Aminu Isa da iyalai da abokan arzikin dalibai na daga cikin maharta taron.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara