Labarai
Majalisar Jigawa Ta Isa Roni A Ci Gaba Da Rangadin Kananan Hukumomi
Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar.
A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati.
Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher domin tabbatar da bin tanade tanaden kashe kudaden gwamnati kamar yadda ya kamata.
Alhaji Aminu Zakari ya kara da cewar a rana ta biyu kwamatin zai duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Roni ta gudanar daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu sannan a karbi rahoton Yan kwamatin wadda hakan zai bada cikakkiyar fahimta game da halin da karamar hukumar ta ke ciki.
Kazalika, yace ziyarar za ta bada damar ganawa tsakanin ‘yan kwamatin da bangaren zartaswa da na kansiloli da ma’aikata domin karfafa wanzuwar dabi’ar aiki tare da kuma kyakkyawar alaka a tsakanin bangarorin karamar hukumar.
A jawabin sa na maraba, shugaban karamar hukumar Roni Dr. Abba Ya’u, ya bayyana amannar cewar ziyarar kwamatin za ta kawo gyara wajen gudanar da mulkin kananan hukumomi.
Dr. Abba ya kuma bayyana kudurin sa na aiki da shawarwarin kwamatin domin kawo cigaban karamar hukumar.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
