Labarai
Gobara Ta Babbake Wani Gida Mai Dakuna Hudu A Jihar Kwara
Wata gobara da ta taso dalilin wutar lantarki ta lalata wani katafaren gida mai dakuna hudu a unguwar Orisunbare da ke unguwar Amoyo a jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kwara Hassan Adekunle ya fitar, ya ce hukumar kashe gobara ta jihar ta samu kiran da aka yi ta samun rahoton barkewar gobara a gida mai lamba 35 a yankin Orisunbare.
A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobarar sun sami wani gida yana cin wuta gangaa ba tare da bata lokaci ba jami’ai suka shiga aikin sui, inda suka nuna kwarewa, jajircewa, da kuma kwarewa.
Sanarwar ta bayyana cewa, saboda jinkirin bayar da rahoto, gidan ya riga ya sami matsala sosai kafin isowar su.
Sanarwar ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wani karin wuta da aka yi, inda ta kara da cewa kasancewar kayan dake cin wuta cikin sauri na da dama a cikin gidan ya taimaka wajen kara ruruwar wutar.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John, ya jaddada mahimmancin bin matakan kiyaye kashe gobara domin kaucewa faruwar haka nan gaba.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
