Fasaha
Gwamnatin Tarayya Ta Nanata Kudurin Koyawa Matasa Sana’o’in Hannu
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na horar da matasa sana’o’i daban-daban a fadin kasar nan.
Sakataren Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci, Dokta Yakubu Adam Kofar Mata, ya bayyana haka, a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan mahalarta shirin “Skill to Wealth” na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Kano.
Dokta Kofar Mata ya jaddada cewa, makasudin bayar da horon shi ne don cika sabbin alkawurran da gwamnati mai ci ta dauka na karfafa matasa.
Shirin bayar da horon na da nufin wadata matasa sana’o’in da za su iya dogaro da kansu da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.
Ko’odinetan shirin na Jiha Dokta Mahdi Isa ya bayyana cewa mahalarta taron 189 daga shiyyar Arewa maso Yamma suna samun horo kan aikin noma, gyaran injinan mota da sabunta makamashi.
Ya ce bayan kammala horon, za a baiwa mahalarta taron da kayayyakin fara kasuwanci domin su fara sana’o’insu.
An tsara shirin horarwa ne domin magance matsalar rashin aikin yi da fatara a tsakanin matasa a kasar.
Isa ya kara da cewa, ta hanyar koyon sana’o’i a bangarori daban-daban, za a ba wa mahalarta taron kwarin gwiwar zama ‘yan kasuwa da kuma ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin kasa.
“Kwarin gwiwar da gwamnatin tarayya ta yi na karfafa wa matasa gwiwa ta hanyar koyon sana’o’i mataki ne mai kyau.
“Shirin horar da ”Skill to Wealth” wata shaida ce ga sabbin manufofin gwamnati, da ke da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman matasa.”
Cover/Abdullahi jalaluddeen/Kano
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
