Labarai
NUJ Ta Kafa Kwamitin Ladabtarwa A Jigawa
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa.
A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne zai jagoranci Kwamitin Ladabtarwar tare da Kwamared Mati Ali, da Dr. Musa Idris Barnawa da Yusuf Sulaiman a matsayin mambobi, yayin da Muhammad Askira Musa zai kasance Sakataren kwamitin.
Sanarwar ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida, warware matsalolin rashin ladabi ko sabawa doka cikin aikin, da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin jarida a jihar Jigawa.
Haka kuma kungiyar ta sanar da kafa kwamitin ilimi da horaswa mai mambobi 7, wanda Kwamared Sani Labaran Salisu zai jagoranta.
Mambobin kwamitin sun hada da Garba Yakubu, Ado Lurwan, Aliyu Dangida, Mustafa Namadi da Balarabe Sani, yayin da Shuaibu Aliyu zai kasance Sakataren kwamitin.
Kwamared Aisha Abba Ahmed ta bayyana cewa an dora wa wannan kwamiti alhakin karfafa gwanintar ‘yan jarida ta hanyar horaswa, taron bita da shirye-shiryen ci gaban aikin su a kai a kai.
Shugaban kungiyar ta NUJ reshen Jigawa, Kwamared Ismail Ibrahim Dutse, ya jaddada cewa kafa wadannan kwamitoci ya nuna kudurin kungiyar wajen karfafa kwararru, gaskiya da inganci a cikin aikin jarida.
Majalisar ta kuma bukaci dukkan mambobi da su ba da cikakken hadin kai ga kwamitocin domin cimma burinsu na ci gaban kungiyar da aikin jarida baki daya.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
