Labarai
Max Air Zai Yi Jigilar Alhazan Jigawa A Ranakun 20 Da 21 Ga Watan Mayu
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu.
Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar hukumar Jin dadin alhazan jihar Jigawa dake Dutse babban birnin jihar.

A cewarsa, ana sa fara jigilar maniyatan jihar zuwa kasar Saudi Arabia a ranar 20 da kuma 21 ga watan Mayun 2025.
Ya ce jirgin Max air zai yi sawun farko da maniyata su 550 zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayu.
Mr Anderson yace a ranar 21 kuma, jirgi na biyu zai dauki maniyata 400 zuwa kasar Saudi Arabia.

Yayi nuni da cewar,jami’an kamfanin za su iso Dutse a ranar 19 ga wata domin kammala duk wani shiri na jigilar maniyatan.
Ya kuma ce kamfanin max air zai tabbatar da ganin an yi jigilar maniyatan cikin kwanciyar hankali domin sauke nauyin da aka dora masa.
Shi ma a nasa jawabin, wakilin hukumar aikin hajji ta kasa mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Alhaji Salisu Gaya ya ce hukumar za ta tabbatar da ganin an yi jigilar maniyatan Jihar Jigawa cikin tsari.

A don haka, ya kuma bukaci maniyyatan da su kiyaye da ka’idoji da kuma dokokin kasa mai tsarki domin kare kima da kuma martabar kasa Najeriya.
A jawabinsa, Darakta Janar na hukumar Jin dadin alhazan jihar jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo yace hukumar ta raba dukkannin kayayyakin aikin hajji ga maniyyata ta hannun shugabannin shiyya-shiyya na hukumar.
Ya kara da cewar, hukumar ta kuma kammala aiki akan takardun biza na maniyyata da yi musu allurar rigakafi da kuma tanadin kudaden guzuri wato BTA.

Alhaji Ahmed Umar Labbo yace makasudin gudanar da taron masu ruwa da tsakin shi ne, domin bibiyar shirye-shiryen da suka yi na samun nasarar aikin hajjin bana dake tafe.
Labbo, ya kuma bayyana cewar, hukumar ta biya bashin naira miliyan dubu 3 da miliyan 360 da Gwamnatin jihar ta bata rance domin sayen kujerun aikin hajjin bana.
Ya Kara da cewar, rancen kudin ya matukar taimakawa hukumar wajen tare kujerun maniyyatan jihar a hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON.
Kazalika, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da yake baiwa hukumar a kowanne lokaci.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
