Fasaha
An Horas Da Likitoci Akan Magance Tsananin Zazzabin Cizon Sauro
Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.
Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da wuri da kuma gaggauta magance cutar zazzabin cizon sauro, musamman a cikin mutane masu rauni kamar yara ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu.
A cewarsa shirin ya kasance wani bangare na faffadan kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar, gami da shirye-shiryen yakin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na 2025 (SMC).
Dokta Fakayode ya bayyana cewa horon zai kunshi zuwa gida-gida da maganin rigakafin zazzabin cizon sauro ga yara ‘yan watanni 3-59 a fadin kananan hukumomi 11 da suka cancanta a jihar Kwara.
Ya yi nuni da cewa har yanzu cutar zazzabin cizon sauro ta kasance babbar barazana ga lafiyar al’umma a Najeriya da jihar Kwara.
Dokta Fakayode ya yaba wa gwamnatin jihar bisa jajircewarta na kawar da cutar zazzabin cizon sauro da kuma saka hannun jarin da yake ci gaba da yi wajen karfafa karfin asibitoci a duk matakan kulawa.
A nata jawabin shugabar shirin na sashin zazzabin cizon sauro, Alhaja Latifat Abdullahi, ta bayyana jin dadin ta ga likitocin da suka halarci wannan taro kan sadaukarwar da suka yi a wannan fanni.
Ta jaddada mahimmancin ci gaba da haɓaka ƙwararru don samun ingantaccen sakamako na kiwon lafiya, ta ƙara da cewa ya kamata likitocin su yi amfani da sabbin dabarun da suka samu a aikace.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
