Kasuwanci
An Bayyana Filin Jirgin Sama Minna a Matsayin Mafita Ga Jiragen da ke sauka Abuja
A hukumance gwamnatin tarayya ta ayyana filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu dake Minna a matsayin mafita ga jiragen dake sauka Abuja.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a yayin bikin kaddamar da jirgin saman na Overland Airways a filin jirgin sama na BAT dake Minna.
Festus Keyamo ya ce ana shirin daukar matakan da suka wajaba kamar su kwastam, shige da fice, ‘yan sanda, NDLEA da sauran su don sarrafa fasinjoji idan filin jirgin Abuja ya samu matsala.
Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago wanda ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da goyon bayan da yake baiwa jihar, ya bayyana cewa wannan nasara wani kokari ne na hadin kai na ganin an farfado da burin jihar a karkashin sabon tsarin mulkin gwamnatin sa.
A nasa bangaren, Wanda ya kafa kuma Manajan Darakta na Kamfanin Jiragen Sama na Overland, Kyaftin Edward Boyo ya bayyana cewa jirgin wani sabon salo ne da aka saya a matsayin sabon tsarin ci gaba tare da sabbin kayan fasahar zamani a bangaren zirga-zirgar jiragen sama yayin da ya ba da tabbacin samar da ayyuka masu inganci.
A nasa jawabin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris Malagi wanda ya yaba da ci gaban da gwamnan jihar Neja ya samu na tabbatar da manyan mafarkai ya kara yabawa ministan sufurin jiragen sama kan gagarumin ci gaba da aka samu a fannin.
Mohammed Idris ya jaddada cewa farashin kayan masarufi na raguwa sannu a hankali a kasar nan, biyo bayan dabarun da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauka na tabbatar da samar da abinci a Najeriya, tare da ba da tabbacin samun kyakkyawar makoma ga ‘yan kasar.
ALIYU LAWAL.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
