Kasuwanci
Kasar Birtaniya na fuskantar karancin ayaba

An fara fuskantar ƙarancin ayaba a manyan kantunan Birtaniya saboda matsalolin sauyin yanayi da ke tarnaki ga samar da ayabar.
Kwararu sun ce masu son cin Ayaba na fama da tsadarta sakamakon yadda sauyin yanayi ke tasiri kan nomanta a sassan duniya.
Wani mai sharhi kan sha’anin tattalin arzikin ayaba a Majalisar Ɗinkin Duniya, Pascal Liu, ya shaida wa BBC sauyin yanayi na janyo tsaiko da yaɗa cututtukan da ke lalata amfanin gona.
Tun a makon da ya wuce ake fuskantar ƙaranci ko rashin ayabar a wasu kantina na ƙasar, bayan guguwar da ta faɗa a tekun Atlantika da ta janyo tsaikon dakon Ayabar ta jirgin ruwa.
Ƙwararru za su yi taro a birnin Rom, domin tattaunawa kan wannan matsala ta ɗaya daga cikin abin da aka fi ciniki da kawo bunƙasar tattalin arziki.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
