Ilimi
AGILE: Gwamnatin Kaduna da Bankin Duniya Na Sauya Rayuwar ’Ya’ya Mata Ta Hanyar Ilimi
Farfesa Bello ya ce gwamnatin jihar ta dage wajen bai wa ’yan mata masu tasowa ingantaccen ilimi da tallafa musu domin su zama masu amfani ga iyalansu da al’ummominsu.
Ya bayyana godiyarsa matuka bisa gudunmuwar da Bankin Duniya ke bayarwa, yana bayyana aikin AGILE a matsayin wani gagarumin sauyi wajen canja ra’ayin al’umma game da ilimin ’ya’ya mata.
“Kalma ba za ta isa ta bayyana yadda muke jin wannan taimako daga Bankin Duniya ba, musamman game da aikin AGILE. Kungiyar aikin a jihar, karkashin jagorancin Maryam Sani Dangaji, ta yi kokari sosai wajen fadakar da iyaye cewa AGILE yana kokarin taimaka wa yarinya ta gane cikakken kwarewarta,” in ji shi.
Farfesa Bello ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kuma kaddamar da wani sabon shiri mai suna “Reaching Out to Out-of-School Children” domin rage adadin yaran da ke waje da makaranta a fadin jihar.
Haka kuma ya bayyana cewa gwamnati ta ware dala miliyan goma sha shida ($16m) domin gina makaranta a ko wace tazarar kilomita daya a yankunan karkara domin karfafa shiga makaranta.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Yankin na Bankin Duniya, Ousmane Diagana, ya jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna kan yadda take jajircewa wajen ganin aikin AGILE ya samu nasara.
Diagana ya jaddada muhimmancin ilmantar da ’yan mata, yana rokon dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da jajircewa duk da kalubale.

“Idan yarinya ta samu ilimi, gaba dayan al’umma ke amfana,” in ji shi, yana mai jaddada bukatar kawar da duk wani cikas da zai hana ‘yan mata cimma burinsu.
Aikin AGILE, wanda Bankin Duniya ke tallafawa, ya zuwa yanzu ya gyara makarantu 665, ya horas da malamai, tare da wayar da kan ‘yan mata game da sauyin yanayi da daukar matakin kare muhalli.
Da take zantawa da Radio Nigeria Kaduna, Daraktar Yanki da ke kula da kasashen Yammaci da Gabashin Afirka kan harkokin Ilimi, Lafiya, Kariya ta Zamani da Jinsin Mata, Trina Haque, ta ce Bankin Duniya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa dukkan ’yan mata masu tasowa sun samu ingantaccen ilimi karkashin aikin AGILE.

Ta kara da cewa Bankin Duniya na aiki kafada da kafada da gwamnonin jihohi da kwamishinonin ilimi domin cimma burin aikin.
Ita ma, Jami’ar Kula da Bin Diddigi na aikin AGILE a Kaduna, Yabai Ayis, ta bayyana nasarorin da aka samu a cikin shekaru hudu da suka gabata.
“AGILE ya gyara makarantu 550 tare da sake farfado da wasu makarantu 115, wanda ya kai jimillar makarantu 665 da suka amfana daga gyare-gyare daban-daban. Haka kuma, an horas da malamai domin inganta koyarwa a duk makarantu na gwamnati a Jihar Kaduna,” in ji Ayis.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da aikin, Success Eliminian, ta yaba wa AGILE bisa sauya dabi’u da al’adun al’umma tare da bunkasa ilimin ’yan mata.

“Aikin AGILE yana sauya tunanin al’umma da al’adunmu. Ya shafe mu ta hanyar ba mu ilmi da da yadda zamu kulada kanmu akan kowane irin kalubale,” In ji ta.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
