Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai  Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40.

A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato.

Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon  bambancin addini da kabila.

Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai domin kawo karshen ramuwar gayya da rikice-rikicen da suka jima suna addabar al’umma.

Ya zaman wajibi a kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin al’umma a Jihar Filato wanda ya samo asali daga rashin fahimta tsakanin kabilu da addinai daban-daban.” In ji Shugaba Tinubu.

Na umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan rikici, da gano wadanda ke da hannu a shirya wadannan ayyukan tashin hankali. Ba za mu amince da wannan barna da hare-haren ramuwar gayya ba. Ya isa haka.

Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba Gwamna Mutfwang da Gwamnatin Jihar Filato goyon baya wajen karfafa tattaunawa, inganta zaman tare, da tabbatar da adalci don magance wannan rikici har abada.

 

Daga Bello Wakili

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara