Labarai
JIBWIS Giwa Ya Bukaci Al’ummar Yakawada su Rike Darussan Al-Qur’ani
Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum.
Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada.

Malam Ibrahim Mustafa ya bayyana jin daɗinsa kan goyon baya da jajircewar al’ummar Yakawada a duk tsawon Tafsirin. Ya jaddada muhimmancin kiyaye darussan da aka koya a cikin Ramadan tare da amfani da su a rayuwa bayan karewar watan mai alfarma.

A nasa jawabin, Sheikh Suleman Abdulkarim Fatika ya nuna godiyarsa ga dukkan mahalarta Tafsirin da suka daure suka halarta tun daga farkon watan Ramadan har zuwa karshensa.
Ya yaba da sadaukarwarsu tare da ƙarfafa su da su ci gaba da neman ilimi da fahimtar addini.
Taron rufe Tafsirin Ramadan din ya samu halartar malamai, shugabannin al’umma, da musulmi mabambanta, wanda hakan ya jaddada mahimmancin koyarwar addini wajen haɓaka haɗin kai da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
COV/Magaji Yakawada
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
