Kasuwanci
Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Da Zamfara
Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025.
A cewar sanarwar mai Magana da aywun rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubukar Abdullahi ya bayyana cewa, a yayin farmakin an kashe ‘yan ta’adda 10 a wata arangama da suka yi a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun.
Ta ce an fara kai farmakin ne a jihar Katsina, inda sojoji suka kai farmakin a kan ‘yan ta’addan a babbar filin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara.
“Hakan ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda 3 tare da ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su.
A halin da ake ciki kuma, a jihar Zamfara, sojojin sun aiwatar da wasu ayyuka a yankin Bagabuzu da ke gundumar Faru, cikin karamar hukumar Maradun wanda ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 7 tare da kwato babur da dai sauransu.
Bugu da kari, an yi nasarar ceto mutane 17 da wani sarkin ‘yan ta’adda ya yi garkuwa da su daga kauyukan Tsibiri da Doka da ke karamar hukumar Shinkafi, kuma a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa, Operation Fansan Yamma na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron al’ummar jihohin Katsina da Zamfara.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
