Labarai
Hukumar Raya Arewa maso Yamma Ta Kai Ziyara Jihar Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta ja hankalin shugabannin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana domin samun goyon bayan gwamnonin shiyyar.
Gwamna Umar Namadi ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada a gidan gwamnati da ke Dutse.

Ya ce, Hukumar Raya Arewa maso Yamma, ita ce mafi girma a cikin shiyyoyin kasar nan, a don haka bai kamata a fuskanci wasu matsaloli ba daga gareta.
Namadi ya bukace su da su mai da hankali da jajircewa, tare da yin aiki da abubuwan da gwamnoni suka sa gaba domin samun nasara.
Tun da farko, Shugaban Hukumar, Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada ya ce sun je ziyarar ce da nufin gabatar da kansu a hukumance da kuma neman tallafi da karfafa gwiwar gwamnati.

A cewarsa, an kafa hukumar ne da amincewar gwamnonin yankin, don haka ya zama wajibi a nemi goyon bayansu.
“Jihar Jigawa jiha cceda ke noma tare da jajircewa, don haka mun ga ya dace mu fara zuwa nan bayan mun ziyarci shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, domin samun goyon baya,” in ji Samaila
Alhaji Sama’ila Yakawada ya ce tuni hukumar ta samu bayanai kan bangarorin hadin gwiwa da jihar Jigawa domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewa.

Ya bayyana Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma a matsayin hukumar da ta fi kowacce hukuma a sauran ayyuka da jihohi bakwai, inda ya ce akwai kalubale da dama.
Shugaban, ya yabawa Gwamna Umar Namadi, bisa kokarinsa na yakar matsalolin da suka addabi al’umma, tun kafin ya hau kujerar gwamnan jihar Jigawa, kamar yadda bayanai suka nuna.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
